Ko ka tsani mutane? To ga abun yi! [8]
|
Hate people Here are the jobs for you] [9]
|
Tun kafin gari ya waye ne Josh Manheimer ya ke fara aiki kuma cikin tunani mai zurfi.
|
It’s before dawn and Josh Manheimer is already at work and deep in thought.
|
A yau ya duba irin kalmomin da suka da ce a yi amfani dasu wadanda za su zaburadda mutane su keta ambulan domin karanta wasiƙa da zarar an ajiye a kofar dakin su.
|
Today he’s imagining the perfect sentence that will make people tear open an envelope as soon as it hits their doormat.
|
Mutane masu zurfin ciki ba su cika buƙatar a yaba musu ba domin su ƙara himma,
|
Introverts need less praise from others in order to thrive,
|
kuma mutane ne masu matuƙar tunani a duk lokacin da suke yanke shawara.
|
show better attention to detail and are more conscientious decision makers.
|
A gidan gona dake Vermont a ƙasar Amurka, Manheimer ya rubuta abun da ya kira "tarkacen saƙonnin email".
|
From an isolated farmhouse in Vermont in the US, Manheimer writes what he unashamedly calls “junk mail”.
|
Shi dai ya na daga cikin wadanda suka shahara a duniya, domin da zarar ka latsa kalmar "direct mail copywriter" a manhajar matan-bayi-baya-bata, zaka ga sunansa ya fito a sama.
|
And he’s one of the best in the world. Just Google “direct mail copywriter”. His name pops up at the top.
|
Ya ce "wannan shine aikin daya fi dacewa da mutumin dake da zurfin ciki."
|
It is, he says, the perfect job for an introvert.
|
Koda yake ba wai baya yin magana bane, ya kan isar da sako ta hanyar email, domin bai taba haduwa da abokan huldarsa ba.
|
Not that we’ve actually spoken. We communicate only by email. He never meets his clients.
|
A kowane lokaci yafi son ya fita waje yana riƙa tafiya tare da karensa ko kuma ya riƙa ba dawakai abinci. "
|
He’d far rather be out walking his dog or feeding the horses.
|
Ya ce ina jin kaina tamkar diyar barewa ce da ta bace a dokar daji"
|
“I do like people,” he says. “But I don’t function well in organisations with politics. I’m like a baby deer, lost and helpless.”
|